Wani Ɗan Sanda Ya Harbe Surukinsa Ya Kashe Ƴan Sanda 6 Saboda Matarsa

Ɗan sanda ya buɗe wa surukinsa wuta, ya kuma harbe wasu ƴan sandan kwantar da tarzoma shida, har lahira kan saɓani da iyalinsa.

Bayan buɗe wutar, Ɗan sandan mai muƙamin Sajan, ya ƙona gidaje da dama, saboda rikicin da yake da matarsa a barikin ƴan sanda da ke Kwalejin Ƴan Sanda a Maiduguri, Jahar Borno, a daren Alhamis.

KARANTA WANNAN LABARIN: Tinubu: Najeriya Na Buƙatar Shugaban Da Zai Samar Da Haɗin Kai, Tsaro Da Tattalin Arziki
Majiyarmu da ke da kusanci da iyalan ta ce, “Ya harbi mutane, shida daga cikinsu ƴan sandan kwantar da tarzoma ne kuma sun rasu, wasu biyu kuma ana jinyar su a Asibitin Ƙwararru.

“Ya harbi surukinsa, sannan ya ƙona jerin gidaje hudu, kowannensu iyalai takwas ne a ciki.”

Wani maƙwabcinsa ya ce tun lokacin da ma’auratan suka samu matsala, maƙwabta suka yi ta ƙoƙarin sasanta su amma mutumin ya ƙi.

Wata majiya a barikin ta ce, “Sajan din da matar suna rikici, shi ne ta shaida wa iyayenta cewa yana dukan ta, har ta kwashe kayanta daga gidansa.

“A sanadiyyar kwashe kayan da ta yi saboda yadda ta ce yana musguna mata ne ya buɗe wa mutane wuta ranar Laraba da dare.”

Wani babban Ɗan sanda a barikin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar wa Majiyar mu faruwar lamarin.

Ya ce, “Suna yawan rikici da matarsa, mu da matan wasu manyan hafsoshinmu mun sha kokarin sasanta su, mun sha yi mishi magana, ba ya ji.”

Ya bayyana cewa bayan matar ta kwashe kayanta ne mijin ya sha alwashin sai ya kashe mutane, idan har ba ta dawo ba.

Ya ce daga baya an yi nasarar tsare ɗan sandan, bayan da ya yi aika-aikan.

Wata majiyar da ta tsallake rijiya da baya ta shaida wa wakilinmu cewa Sajan din, “Ya zo gidanmu ya fara harbe-harbe, shi ne muka tsere, saboda yana barazanar cewa zai kashe kowa duk a huta.”
Aminiya ta gano cewa a halin yanzu Sajan din yana tsare a Sashen Binciken Manyan Laifuka a Hedikwatar ’Yan Sanda ta Jihar Borno.

Wakilin Majiyar mu ya yi kokarin samun karin haske daga hukumomin ’yan sandan jihar, amma abin ya faskara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram