2023: Bayan Na Yi Shekaru 8 Na Wa’adin Mulkina, Zan Miƙa Ma, Dan Sliyasar Da Ya Fi Kowa Masoya — Cewar Tinubu

Tsohon Gwamnan Jahar Lagos, kuma Jagoran Jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana cewar idan aka zaɓe shi a matsayin Shugaban Ƙasa a Shekarar 2023, zai yi Mulki ne na Shekaru 8.

Tinubu, wanda Ɗan takarar Shugaban Ƙasa ne a Jam’iyyar APC, bayan cewa zai yi wa’adi biyu, zai kuma miƙa ma Mulki ga ɗan Siyasa da san abinda yake yi, da Masoya masu tarin yawa.

KARANTA KUMA: Ana Barazanar Bindige ‘Yan Najeriya A Ukraine

Majiyar Jaridar Jakadiya ta ruwaito cewa, Jigon Jam’iyyar APC, ya bayyana haka a Akure, Babban Birnin Jahar a daren ranar Juma’a, a lokacin da yaje neman shawara akan Takarar sa ta Shugabancin Ƙasa ga Masu riƙe da Sarautun gargajiya a Jahar.

Tsohon Gwamnan Jahar Lagos ya cigaba da cewa idan ya zama Shugaban Ƙasa a Shekarar 2023, zai ɗora ƙasar a turba mai kyau.

A lokacin da yake nuni rashin jindaɗi na yadda har yanzu Najeriya bata kai maƙurar daya kamata ace taje, Tinubu ya bayyana cewa, bawai zai bayar da ɗimbin ayyuka kaɗai ba, zai tabbatar da cewa an samar da Masana’antu a faɗin Ƙasar.

“Idan nayi Shekaru takwas ina Mulki, zai miƙa wa Dan Siyasa mai goge, da kaifin basira, mai tarin Masoya, wanda zai cigaba daga inda na tsaya bayan na kammala.

“Abin tausayi ne ace ƙwado Najeriya bazata iya samar wa ba. Zan maido da Najeriya Ƙasa mai kyawu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram