Ana Barazanar Bindige ‘Yan Najeriya A Ukraine

Wasu daliban Najeriya da ke karatu a kasar Ukraine sun koka kan yadda sojojin kasar suka yi barazanar bindige su a yayin da suke kokarin guje wa mamayar da Rasha ke yi wa kasar.

Wani dalibi da ke karatun likita, Adebowale Oduola, ya fada wa kamfanin dillancin labaru na Reuters jim kadan da saukar sa Abuja a ranar Juma’a cewa, shi da wasu abokai na kokarin shiga wani jirgin kasa ne a lokacin da sojojin suka nuna masu bakin bindiga tare da umartar su da su koma baya.

KARANTA KUMA: PDP Ta Yi Wa Mutanen Katsina Alkawari Cewa Idan Ta Ci Mulki Ba Wanda Zai Kara Sa Matattar Riga Ko Kayan Gwanjo

Sojojin sun fada masu cewa suna kyale mata ma su ciki ne kadai su shiga jirgin daga birnin Lviv zuwa kan iyakar kasar Poland, amma duk da haka a cewar su, sun ga ana hana matan masu ciki ‘yan Afirka shiga jirgin.

Kamfanin Reuters din ya ce, ba zai iya tantance ainihin yawa ko kasashen daliban Asiya da Afirka da aka fitar daga jiragen kasa ko aka tare a kan iyakoki sannan aka mayar da su bayan dogayen layuka.

Kungiyar hadin kan kasashen Afirka, AU, ta nuna damuwar ta a kan abin da ke faruwar, sannan ita ma hukumar kula ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, ta bukaci kasashen da ke makwabtaka da Ukraine da su bude iyakokin su ga ‘yan Afirkan.

Tuni dai jirgi na biyu dauke da ‘yan Najeriya su 180 ya sauka a Abuja da yammacin ranar Juma’a, 4 ga watan Maris, 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram