Duk Ɗalibin Da ya Karya Dokoki Ba Zamu Yi Hulɗa Da Shi Ba A UTME na 2022 — JAMB

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandare, JAMB ta ce za ta cire sunan duk wani dillali da wakili da ya karya dokoki Haɗaɗɗiyar Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba Da na Sakandare, UTME na 2022.

Rijistaran hukumar, Is’haq Oloyede, ne ya baiyana haka a Ibadan a yau Asabar lokaci da ya kai ziyarar gani-da-ido na aikin rijistar jarrabawar.

Oleyede ya nuna jin daɗi da gamsuwa a bisa yadda aikin yin rijistar ke tafiya a wasu cibiyoyi.

 

Ya koka da cewa tsoma hannu da iyaye su ke yi ne ya ke kawo naƙasu a aikin rijistar da ke gudana a halin yanzu.

Ya ce a kwai cibiyoyi da aikin ya ke tafiya yadda a ke so, amma aikin da ke gudana cibiyar da ke cikin Jami’ar Ibadan ya fi kowanne kayatar wa.

“Za mu zare sunayen wasu dillali da wakilai a wasu cibiyoyin sabo da idan ba ka bi ƙa’idojin mu ba, to ba ka da damar da za mu yi maka rijista,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram