Gwamnatin Lagos Ta Rufe Cibiyar Taron Da Aka Rarraba Man Fetur Kyauta

Gwamnatin Jahar Lagos ta kulle wajen wuni wuri da ake gudanar da taro Havillah, bayan bincike akan wani bidiyo da yayi yawo dake nuna ana bada jarka da Man Fetur a matsayin Tukuici a wani bikin daya gudana a wajen.

Kafin nan, wata yarinya mai suna Chidinma Pearl Ogbulu ta janyo hankulan ƴan Najeriya a Kafafen Yaɗa Labaru da kyautar Man Fetur a taron data shirya a matsayin Erelu Okin.

Bidiyon da aka ɗauka a taron ya nuna wata jarka mai cin kilogaram 10 ɗauke da Man Fetur a ciki an tane je shi ga baƙin da suka zo domin taya ta murna.

Dayake maida martani akan wannan bidiyon, Kwamishinan Yaɗa Labaru da Dabaru Gbenga Omotoso, yace “babu kokwanto wannan al’amarin akwai hatsari a cikin sa, kuma yana iya haifar da mutuwar mutane da dama da rasa dukiyoyi. Ya karya dukkanin Dokokin Kariya a wurin.

“Gwamnatin Lagos ta hanyar Hukumar Kiyaye Lafiyar Al’umma tana bincike akan lamarin, kuma zata tabbatar cewa duk waɗanda hakan ya faru dasu, zasu ɗanɗana kuɗar su.

Waɗanda suka shirya taron, sun lura da cigaba da ake samu na ƙarancin Man Fetur, a yayinda Dogon Layi a gidan Mai ya cika a faɗin Ƙasar.

“Gwamnatin Lagos ta kulle gurin da akayi taron.

Babban Mai Taimakawa Gwamnan akan Kafafen Sadarwa na Zamani Jubril Gawat ya ƙara dacewa Kwamishinan Ƴan sanda na Jahar Lagos ta bada umarnin a Kamo waɗanda aka gani sun shirya taron.

A saƙon Kafar Sadarwa ta WhatsApp, Mai Taimakawa Gwamnan yace “Gwamnatin Jahar Lagos ta hanyar Hukumar Kiyaye Lafiyar Al’umma da bada agajin gaggawa ta rufe wajen taro na Havillah Event Centre dake Oniru, sakamakon karya dokar kiyaye Lafiyar Al’umma, na bada kyautar Man Fetur, a yayinda Kwamishinan Ƴan Sanda ta bada umarnin a kamo su

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram