Mai Martaba Sarkin Katsina, Abdulmunini Kabir Usman ya bayyana tsohon Gwamnan jihar Legas kuma mai son tsayawa takarar Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a matsayin cikakken dan jihar Katsina mai lasisi wanda kuma ke da dadaddiyar dangantaka da masarautar.
Kakaki Network ta nakalto daga majiyarta, cewa sarkin ya bayyana haka ne a jiya Juma’a yayin da ya karbi bakuncin wata tawagar tallata takarar Tinubu da ta kai masa ziyara a fadarsa.
Duk Ɗalibin Da ya Karya Dokoki Ba Zamu Yi Hulɗa Da Shi Ba A UTME na 2022 — JAMB
Sarkin ya ce fiye da shekaru 30 da suka wuce, tsohon Gwamnan jihar Legas din ya na dan kyakkyawar alaka da masarautar tun lokacin da mahaifinsa, marigayi Muhammadu Kabir Usman ke kan karagar mulki.
Hakazalika ya kuma jaddada goyon bayan sa ga tafiyar siyasar ta Bola Ahmed Tinubu.