Likitan Gargajiya Ya Rataye Kansa A Jahar Benue

  1. Mazauna Mazaɓar Mbakuha dake Ƙaramar Hukumar Ushongo ta Jahar Benue, sun kasance cikin ruɗani, bayan wani Likitan Gargajiya mai Shekaru 42 ya kashe kansa ta hanyar rataya kan sa.

Likitan Gargajiyan da ake kira da Terhemen Iorbee, a kwanakin baya an bada cigiyar sa, bayan ɓata da yayi, kafin daga bisani a ga gawar sa a wani icce rataye.

Lamarin, wanda ya faru a cikin hutun mako, yadai taɓa zuciyar mazauna yankin.

Duk da ba’a samu wata takarda wadda zata bayyana dalilin dayasa ya kashe kansa, mazauna garin sun ce wanda ya mutum ya nuna wasu ɗabi’u a ƴan kwanakin da suka wakana.

“Babu wani abu da za’a iya tabbatar da dalilin daya haddasa kashe kan, illa wasu ɗabi’u daya riƙa nunawa a ƴan kwanakin nan.

“Likitan Gargajiya ne, kuma yanada mata uku, da ƴaƴa huɗu,” kamar yadda mazauna garin suka bayyana.

A lokacin da aka tuntuɓi Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Catherine Anene ya tabbatar da mutuwar Likitan Gargajiyan ta hanyar rataye kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram