Rikicin Siyasa Ya Jikkata Mutane Da Dama A Filato

Rahotanni sun bayyana cewa an jikkata mutane da dama a yammacin ranar Asabar a Sabon Gida hedikwatar karamar hukumar Langtang ta Kudu a jihar Filato bayan wani rikici da ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC da na PDP.

Lamarin dai ya faru ne a lokacin da ake bikin ranar sake tsugunar da ‘yan kabilar Tarok a jihar.

Wani ganau mai suna Lanchang Timpil ya bayyana cewa rikicin ya barke ne a lokacin da tsohon shugaban jam’iyyar Langtang ta Arewa Ubandoma Laven wanda dan jam’iyyar PDP ne ya isa wurin da ake gudanar da bikin kuma babban malamin ya gayyace shi zuwa wajen zaman manyan baki.

An ce shugaban na yanzu, Vincent Bulus Venman, dan jam’iyyar APC, bai ji dadin gayyatar ba.

Timil ya ce shugaban ya je wurin tsohon shugaban, kuma “wannan ya haifar da tashin hankali.”

“An tabbatar da fada tsakanin matasan kuma mutane da dama sun jikkata,” in ji shi.

Kokarin samun Laven ya ci tura domin bai amsa kiran da aka yi masa ba, ko kuma ya amsa sakon da aka aike masa har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Sai dai Venman da aka tuntube shi, ya ce ba zai iya magana ta wayar tarho ba game da lamarin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram