Jakadiyar Ukraine a Amurka ta kira kasar Rasha da ‘yan ta’adda’.
Jakadiyar Ukraine a Amurka Oksana Markarova, ta kira Rasha a matsayin kasar ‘yan ta’adda saboda mamayewar da ta yi a Ukraine.
Ta fadi haka ne a wata hira da Jaridar Fox News a ranar Lahadi.
Ta kuma bukaci Amurka da ta taimakawa Ukraine da makamai da sauran abubuwan taimako.
“Wannan kasa ce ta ta’addanci kuma ya kamata mu dauki Rasha a matsayin ‘yan ta’adda,” in ji Markarova, a cewar Sky News.