“Yadda Ma’aikatar Shari’a Ta Najeriya Ta Gaza Yiwa Mahaifina Adalci” – Bello Turji

Jagoran Yan bindiga a jihar Zamfara, Bello Turji, ya yi ikirarin cewa mahaifinsa ya shiga kotu tsawon shekaru amma ya kasa samun adalci.

A tattaunawarsa da Mataimakin Babban Editan Jaridar Daily Trust, Abdulaziz Abdulaziz, Turji ya yi magana kan batutuwa da dama.

KARANTA KUMA: Gobara Ta Ƙone Kayaiyakin Tallafi Na Miliyan 18.5 A Hukumar SEMA Ta Kano

Shahararren dan fashin ya kuma ce zai iya tuntubar wasu gungun ‘yan bindiga da ke addabar yankin Arewa maso Yamma, domin a tattauna Kuma a samu zaman lafiya a fadin yankin Baki daya.

A cewar Tirji “Mahaifina ya shiga shari’a har na tsawon shekaru bakwai a kotu kan batutuwan da suka shafi rigimar hatsi kawai! Kuma ya bi duk kotuna har da ta Abuja do in samun adalci.”

“Na rantse da Allah a gidanmu muna da shanu sama da 100, amma an bar mu da wadanda basufi guda 20 ba kawai. Kuna iya tabbatar da duk abin da na fada muku daga sarakunan gargajiya. Zan iya kawo wanda ake tuhuma (a cikin karar mahaifina); shari’ar ta dau shekaru, tun ina karami na dade har na girma a na shari’ar. Haka nan kuma babu inda iyayenmu ba su je su Nema mana adalci ba a kan kwace mana filayenmu, Amma abun ya citira.”

“Duk wadannan batutuwan Sarkin Shinkafi ya sansu. Ya san iyayenmu tsawon shekaru kuma ba ’yan fashi ba ne. Ba a taba kai masa rahoton sata ba. Amma hakannan aka sace mana shanunmu, ak kashe ’yan’uwanmu, aka mayar da mu marasa komai. Babu wata hukuma da za ka kai kara domin samun hakkinka, babu mai bimaka hakkinka. Za ka iya yin kuka har abada? Za ka gaji da kuka da neman mafita. Kuma wannan ita ce matsalarmu a kasar nan. Ba mu da wata bukata face dakatar da kashe mutanenmu.” inji Bello Turji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram