Ba Gaskiya Ba Ne Batun Karɓar Ragamar Shugabancin APC – Gwamna Abubakar Sani

Gwamna Abubakar Sani Bello na Neja ya musanta karbar ragamar shugabancin jam’iyyar APC a matsayin mai rikon kwarya da tsare-tsare na musamman (CECPC) kamar yadda wasu kafafen yada labarai ke hasashe.

Bello ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya jagoranci taron jam’iyyar APC CECPC a sakatariyar jam’iyyar ta kasa a Abuja ranar Litinin.

Ya ce ya gana da shugaban jam’iyyar APC na jihohi tare da kaddamar da wasu sabbin zababbun shugabannin jihohi.

“Shugabannin Jihohin sun yi rantsuwar kama aiki a yau kuma mun tattauna kan ci gaban da aka samu a babban taron kasa mai zuwa da kuma abin da ya kamata a yi nan gaba domin mu cimma ranar 26 ga watan Maris na gudanar da babban taron,” in ji shi.

Da aka tambaye shi ko wane matsayi ya jagoranta a tarukan, Bello ya ce: “Na jima ina aiki tun lokacin da shugaban (Buni) ya yi tafiya”.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa taron ya samu halartar dukkanin mambobin kwamitin da suka hada da Sakatare, Sanata John Akpanudoedrhe, wakiliyar mata, Misis Stella Okotete, shugaban matasa, Mista Ismail Ahmed da kuma Mista David Lyon.

Majiyar Jaridar Jakadiya ta rawaito cewa wadanda suka halarci taron sun hada da Farfesa Tahir Mamman, Sen. Ali Abba, Sanata Ken Nnamani da kuma Sanata Yusuf Yusuf.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram