Wata Sabuwa: Duk Lalacewar Jam’iyyar PDP Gwara Ita Da APC – Cewar Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyar APC ce mafi lalacewa cikin jam’iyyun siyasa a wannan lokaci.

Tsohon Sanatan ya kuma ce dukda dai itama PDP ɗin ba kanwar lasa bace wajen kama-karya a yanzu, amma dai za a iya cewa gwara-gwara idan a ka kwatanta ta da APC.

Kwankwaso ya yi wannan furuci ne a jiya Lahadi, yayin taron masu ruwa da tsaki na ɗarikar Kwankwasiyya a gidansa dake Kano.

Ya ce wasu “sojojin gona” ne su ke yin kama-karya a PDP, inda ya koka da cewa duk cancantar mutum da haƙƙin sa, zai iya rasa shi ta dalilin waɗannan sojojin gonar.

Kwankwaso ya jadda cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP, amma shirye-shirye sunyi nisa a tsakaninsa da jam’iyyar NNPP.

Kwankwaso yace fita daga jam’iyya da komawa ba illa bane, kuma hakan ma shi ne kwarewa a siyasa.

Ya tuna cewa a shekarar 2018 da su ka yi zaben fidda gwani a Fatakwal, wadanda su ka zo na farko, na biyu, na uku da na hudu, duk sunbar PDP sun dawo, “sai kuma wasu tarkace da suka biyo baya, a cewar Kwankwaso.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram