Dan Bilki Kwamanda ya Shiga Hannu, Kan Bata Sunan Ganduje

An gurfanar da Abdulmajid Danbilki Kwamanda, babban mai goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma na hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari a gaban wata babbar kotun majistare dake Normansland ta jihar Kano.

An gurfanar da Kwamanda a gaban babban alkalin kotun, Aminu Gabari bisa zarginsa da bata sunan gwamnan jihar Kano, Umar Abdullahi Ganduje.

Alwan Hassan Naif, mai taimakawa mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo ne a wata hira da aka yi da shi a makon da ya gabata ya zargi shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni da karbar cin hanci daga gwamna Ganduje domin bai wa shugaban jam’iyyar na jihar Kano Abdullahi Abbas takardar shaidar dawowarsa kan mukamin.

Akan haka ne Danbilki Kwamanda ya zagaya wani gidan rediyo na cikin garin Kano, inda ya zargi Gwamna Ganduje da bai wa Buni cin hanci don samun takardar shaidar dawowar Abbas kan mukaminsa.

Kazalika an kama shi ne bayan hirar.

Ko da yake Kwamanda ya musanta zarge-zargen da ake masa, bisa cewa kawai ya bayyana ra’ayinsa ne kan abin da hadimin Osinbajo ya ce, sai dai har kawo hada wannan rahoton yana nan a gaban Kotun Majistare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram