Hatsarin Mota ya Kashe Wani Yaro da Wasu Mutum 6 a Jihar Neja

Matafiya 7 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Suleja zuwa Minna.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ce hatsarin da wata motar bas mai dauke da mutane 18 ta yi hadarin ne da misalin karfe 7 na yammacin ranar Litinin a kauyen Farin-Doki da ke karamar hukumar Paikoro a jihar Neja.

Abiodun ya ce, “A ranar 07/03/2022 da misalin karfe 1910, an yi hatsarin mota guda daya tilo a kauyen Farin-Doki, ta Paiko kan titin Suleja zuwa Minna wanda wata motar bas kirar Toyota Mai lamba. KNC 297 ZU wanda wani mutum Mai suna Ilyasu Bala ke tukawa.”

Ya kara da cewa motar da ta taso daga Katshina na kan hanyar zuwa Legas ne a lokacin da direban motar ya rasa shanyo kan motar a Farin-Doki ta Paiko sakamakon wata matsala da ta samu.

“Abin takaici, motar bas din ta afkawa cikin wani Ramin, yayin da direban da wasu Mutum shida suka mutu nan take, wasu fasinjoji takwas sun samu raunuka daban-daban,” in ji kakakin ‘yan sandan.

Ya ce tawagar ‘yan sandan da ke sintiri a yankin Paiko ta hanzarta zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti mafi kusa domin kula da lafiyarsu, yayin da aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa na asibitin kwararru na Ibrahim Badamasi Babangida.

Wani ganau ya ce wadanda suka mutu maza biyar ne, mace daya da yaro daya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram