Wata Sabuwa: Babu wani alƙali da ya ke da ikon cire ni da ga Gwamna – Umahi

Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi ya yi jifa da hukuncin da Babbar Kotu ta yi na tsige shi da ga kan kujerar sa, inda ya ce har yanzu shi ne gwamna.

Umahi ya yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalin su domin zai rusa wannan hukuncin a Kotun Ɗaukaka ƙara.

Umahi, wanda ya suffanta hukuncin da Mai Shari’a Inyang Ekwo ya yi a yau Talata a matsayin zalunci, ya ce tuni ma ya kai ƙorafin alƙalin ga Hukumar kula da Harkokin Alkalai ta Ƙasa, NJC.

A cewar sa kotun ba ta da ƙarfin da za ta iya cire shi sabo da a kwai rigar kariya da kundin tsarin mulki ya bashi ta cewa ba za a kai shi kotu ba.

Umahi ya yi nuni da cewa akwai wasu shari’o’i a kan sauya sheƙa da wata babbar kotu a Ebonyi ta yi ga kuma na Zamfara inda gwamnan ya samu nasara a kotun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram