Zaɓen Gwamnan Osun: Ademola Adeleke ya zama Ɗan takarar Jam’iyar PDP

Shugaban zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a jihar Osun Lawrence Ewhrudjakpo ya bayyana Sanata Ademola Jackson Adeleke a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben gwamna da za a yi a ranar 16 ga watan Yulin shekarar nan

Ya ce Ademola Adeleke ya samu kuri’u 1,887 a zaben fidda gwani na Yan takarar gwamna a jam’iyyar.

Da yake mikawa Adeleke takardar shedar kasancewa Mai tsayawa Takarar a inuwar jam’iyyar PDP, Ewhrudjakpo ya bayyana cewa wakilai 1,916 ne suka kada kuri’ar su a zaben, yayin da aka Sami kuri’u 24 da ba su inganta ba.

Kamar yadda aka sanar, Dele Adeleke, ya Sami kuri’a daya 1; Dotun Babayemi, 0; Akin Ogunbiyi, 0; Fatai Akinbade, 0 da Sanya Omirin, 4; .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram