Buhari Ne Ya Bada Umarnin A Cire Mai Mala Buni Daga Rikon Jam’iyyar APC – El-Rufa’i

Gwamnan jahar Kaduna, malam Nasiru El-Rufa’i ya bayyana cewa, Shugaba Muhammadu Buhari ne ya goyi bayan cire gwamnan Yobe Mai Mala Buni a matsayin shugaban riko na APC

El-Rufa’i ya ce haka ne a wata hirar da kafar talabijin ta Channels ta yi da shi ranar Talata, ya ce gwamnan Neja Sani Bello ya samu goyon bayan Buhari da kuma gwamnonin APC 19.

BBC Hausa, ta ce, sannan ya ce Buhari ne ya ce a cire gwamnan Yobe Mai Mala Buni.

“Buhari ne ya bayar da umarnin a cire shi kuma aka aiwatar, yanzu gwamna Bello ne ya gaje shi,” kamar yadda El Rufai ya bayyana.

Ya ce Mai Mala Buni wanda ba ya ƙasar zai dawo ne a matsayin gwamnan Yobe amma ba matsayin shugaban jam’iyyar APC ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram