Bai Kamata Ku Rinka Aibata Musulmi Ba Kuma Ba Ku San Kaddararku Ba – In Ji Nafisa

Nafisa Ishak wadda ta yi wani bidiyo kilif da ya yi yawo a kafafen sada zumunta game da raddi da ta mayar ga Sheikh Aminu Daurawa bayan da ya ce gaban mace ba abin birgewa ba ne, ta fito ta bai wa malam hakuri da kuma sauran musulmi baki daya.

Ta fito ne a cikin wani hoton bidiyo tana bada hakurin, inda ta ce ta yi murya tana bada hakurin amma ta ga kamar Jama’a ba su gamsu ba.

Nafisa ta ce ita ba ta yi haka ba ne da nufin cin mutumcin malam ko muzanta shi ba.

Ta ce saboda haka kowa ya yi hakuri ya yafe mata.

Ta kuma ce masu zagi da aibatata su daina saboda ba abu ne mai kyau ba, ta kara da cewa babu wanda ya san kaddarar da ke tattare da shi don haka a daina saurin aibata Musulmi in ya yi abinda ba daidai ba.

Ta ce addu’a ya kamata mutane su yi a maimakon zagi da tsinuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram