Bayan daina Hulɗa da Kamfani yayi da Chelsea zata iya buga wasan ta da Norwich ba tare da Hatimi ba

Chelsea ka iya buga wasanta da Norwich batare da Hatimin “3” ba, bayan kamfanin ya janye hulda da kungiyar

Kamfanin sadarwa, Mai tambarin Three (3), a ranar Alhamis ya tabbatar da dakatar da yarjejeniyar daukar nauyin rigar kungiyar Kwallon kafa ta Chelsea nan take da kudin sa ya Kai kimanin fam miliyan 40.

Hakan ya biyo bayan takunkumin da aka sanya wa mamallakin kungiyar ta Blues Roman Abramovich.

Hamshakin attajirin dan kasar Rasha an daskarar da kadarorinsa a Burtaniya sakamakon mamayar da kasarsa ke ci gaba da yi a Ukraine.

Duk da haka, dan shekaru 55 ya ci gaba da musanta duk wata alaka da shugaba kasar ta Rasha Vladimir Putin.

Tambarin na Three (3) a yanzu ba zai sake fitowa a kan rigunan Chelsea da kuma kan allunan talla a kusa da filin wasa Stamford Bridge ba har sai an samu wata sanarwa a nan gaba.

Sun kasance babban mai daukar nauyin rigar Chelsea tun farkon kakar wasa ta 2020 da 2021.

“Mun fahimci cewa wannan shawarar za ta yi tasiri ga yawancin magoya bayan Chelsea da ke kishin kungiyar. Duk da haka, muna jin cewa idan aka yi la’akari da halin da ake ciki, da kuma takunkumin da gwamnati ta sanya, shi ne abin da ya dace a yi,” in ji sanarwar a wani bangare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram