Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya amince da nadin Mista Adamu Yohanna, Dagacin kauyen Tafa Gari, a matsayin mai kula da sabuwar masarautar Dnata da aka kirkiro a karamar hukumar Kagarko ta jihar.
El-Rufai ya bayyana hakan ne ta bakin shugaban karamar hukumar, Mista Nasara Rabo, a wata wasika da kafar yada labarai ta Elanza ta samu a ranar Alhamis.
Idan za a iya tunawa, Masarautar Dnata na daga cikin Sarakuna hudu da gwamnatin El-Rufai ta kirkiro a ranar 1 ga watan Nuwamba, 2021.
Wasikar tana cewa; Na rubuto ne domin isar da amincewar mai girma Gwamnan Jihar Kaduna, Mal.Nasir El-Rufa’i ya nada ka a matsayin mai kula da sabuwar masarautar Dnata ta 3 da gaggawa! har sai an nada babban shugaba.
Sai dai shugaban karamar hukumar, Nasara Rabo ya bukaci sabon mai kula da masarautar da ya kiyaye ka’idojin al’adu tare da samar da zaman lafiya tare da hada dukkan kabilun da ke yankinsa wuri guda.
Ya bayyana cewa an bi matakin ne domin karfafa zaman lafiya a tsakanin al’umma da kabilun da ke cikin masarautar.
An kirkiro sabuwar masarautar ta Dnata ne daga masarautar Jere, inda kogin Jere da Tafa na jihar Kaduna da Neja suka raba.
Wakilinmu ya rawaito cewa akwai gidaje biyar masu mulki a yankin, wadanda suka hada da Kagumi, Gujeni, Idda Dulumi da kuma Chakunwo.