NNPC ta ginawa BUK Katafaren Gini na Naira Miliyan 400

Kamfanin Man Fetur na Ƙasa wato-NNPC a ranar Juma’a ta ƙaddamar tare da miƙa wani sabon Katafaren wuri data gina a Sashen Civil Engineering na Jami’ar Bayero dake Kano.

A cewar Manaja-Darakta na Kamfanin Man Fetur ɗin Mele Kyari, kamfanin ya kashe Naira Miliyan 400 domin gina wurin.

Yace wannan gini, wani ɓangare ne na bada gudunmawa ga cigaban Ilmi a Manyan Makarantun Ƙasar.

Kyari wanda ya samu wakilcin Babbar Daraktar Kamfanin Hajiya Aisha Farida Katagum yace ginin an sanya mashi suna NNPC Complex, domin nuna irin namijin ƙoƙarin da NNPC ke yi domin inganta ilmin manyan Makarantu, da gine-gine domin inganta koyo da bincike.

Tace “wannan ginin an ƙirƙire shi, bayan roƙon da Jami’ar tayi a Shekarar 2018.

“Abubuwan dake cikin ginin sun ƙunshi Azuzuwa, Ɗakin gwaje-gwaje, tiyatar ɗaukar karatu, da wajen ajiye mota da sauran su, inji Katagum.

Dayake jawabi a madadin Shuwagabancin Jami’ar, Shugaban Jami’ar Farfesa Sagir Adamu Abbas wanda ya samu wakilcin Mataimakin sa a ɓangaren ilmi Farfesa Sani Muhammad Gumel ya godema NNPC da wannan gagarumar gudummawa, sai yayi kiran cigaba da haɗin kai a ɓangaren bincike da cigaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram