Ɗalibin Sakandare Ya Kashe Abokin Karatunsa Da Wuƙa A Jahar Akwa Ibom

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Akwa Ibom ta tabbatar da cewa wani ɗalibin makarantar sakandaren gwamnati ta Aka Offit, Samuel Archibong ya caka wa abokin karatunsa, James Elijah wuƙa ya kashe shi har lahira.

Kakin rundunar, Odiko Macdon ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Uyo a yau Asabar.

Ya ce tuni Kwamishinan Ƴan Sanda na jihar, Andrew Amiengheme ya aika rundunar binciken sirri ta musamman zuwa makarantar domin daƙile sake afkuwar lamarin.

A cewar kakakin, ba wannan ne karon farko da a ke yin kisa a makarantu a jihar ba, inda ya ci alwashin cewa rundunar ba za ta zuba ido irin hakan na faruwa ba.

Ya ce Kwamishinan Ƴan Sanda ya nuna ɓacin ran sa kuma ya yi alla-wadai da abin da ya faru.

Macdon ya ƙara da cewa da ga yau rundunar za ta rika tura jami’an ta su rika tabbatar wa kowa ya tafi gida bayan an tashi da ga makaranta.

Mamakin ya tabbatar da cewa za a kama wanda yai kisan kuma zai girba abin da ya shuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram