Likita Na Ya Gaya Man Cewa Shekaru 5 Suka Rage Ma Ni A Duniya – Jarumar Nollywood

Jarumar masana’antar fina-finai ta Nollywood, Kemi Afolabi ta baiyana cewa likitanta ya sanar da ita cewa shekara biyar kacal za ta ƙara yi a duniya ta mutu.

A wata tattaunawa da ta yi da wani dan jarida, Chude Jideonwo, jarumar ta ce tana fama da cutar jeji mai suna lupus.

A cewar ta, likitan ya ce mata cutar ba ta warke wa, sai dai ai ta shan magani har zuwa lokacin da Allah Ya yi.

Afolabi ta baiyana cewa ta kashe sama da Naira miliyan 1 a magani amma har yanzu ba ta samu sauki yadda ya kamata ba.

A cewar ta, likitan na ta yanke mata, “ki tabbata kullum kina cikin ƴan uwan ki sabo da a ƙalla za ki iya ƙara shekar biyar nan gaba,”

Tun a watan Janairu ne Afolabi ta wallafa a shafinta na kafar instagram cewa ta rubuta wasiyya kuma har ta ajiye gurin da za a binne ta a makabarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram