NUC ta amince wa Jami’ar UMYU karantar da Sabbin Kwasa-kwasai 14

Hukumar Kula da Jami’o’in Najeriya NUC ta amince a Karantar da Sabbin Kwasa-kwasai 14 a Jami’ar Umaru Musa Ƴar’adua dake Katsina.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke dasa hannun Daraktan Tsare-tsaren Ilmi na Hukumar Dr. N. B. Saliu, dake da kwanan wata 11 ga watan Maris da aka aikewa Shugaban Jami’ar ta Umaru Musa Ƴar’adua.

Takardar tace “an umarce ni da in shaida maka cewa, Shugaban Hukumar Kula da Jami’o’i ta Najeriya ya amince da fara karantar da Ɗalibai sabbin kwasa-kwasai 14 a mazaunin Jami’ar, wanda zaka iya farawa daga zango na 2021/2022.

Takardar ta ƙara dacewa idan dai zaka tuna, wata tawagar masana da ta kawo maka ziyarar domin duba yanayin Ma’aikata da Kayayyakin Koyo da Koyarwa, a nan Jami’ar Umaru Musa Ƴar’adua.

A Sabo da haka an amince ka fara karantar da waɗannan sabbin kwasa-kwasai 14 kamar haka;

1) MBBS Medicine and Surgery
2) B. Forestry and Wildlife Management
3) B.Ed. Integrated Science
4) B.Sc. Meteorology
5) B.Agric. Agricultural Science
6) B.Ed. Business Studies Education
7) B.Sc. Environmental Management
8) B.Sc. International Relations
9) B.Ed. Primary Education Studies
10) B.Sc. Fisheries and Agriculture
11) B.Sc. Local Government and Development Studies
12) B.Ed. Early Childhood Education
13) B.Sc. (Ed) Computer Science Education
14) B.Ed. Special Education

Sanarwar tace, ba’a amince domin karantar da waɗannan Kwasa-kwasai ba na wucin gadi, kuma sannan dole abu dokokin karantar da kwasa-kwasan kamar yadda aka amince, in Kuma akwai canji to sai Hukumar NUC ta sani.

Haka zalika, takardar tayi kira ga Jami’ar Umaru Musa Ƴar’adua data yi ƙoƙari domin samar da dukkanin Ma’aikata da kayayyakin da ake buƙata domin cigaban gudanar da waɗannan sabbin kwasa-kwasai da aka amince.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram