Rundunar Yan sandan jahar Katsina ta kama wani matashi mai suna Jamilu Sa’idu da take zargi da yunkurin yin garkuwa da wani mutum.
Kakakin rundunar SP Gambo Isah ne ya gabatar da matashin ga manema labarai a shelkwatarsu da ke Katsina.
KARANTA KUMA:NUC ta amince wa Jami’ar UMYU karantar da Sabbin Kwasa-kwasai 14
Matashi Jamilu dai ya kirawo wani ta wayar salula ya yi ikirarin cewa ko dai ya bashi dubu 200 ko kuma ya yi garkuwa da shi.
Bayan binciken jami’an Yan sanda sun samu nasarar kama matashin.
Sai dai da aka tambaye Jamilu ko ya san girman laifin da ya aikata sai ya bada amsa da cewa bai san laifin ya girma haka ba.