Wata Kotu ta yanke hukunci ga wanda ya sace Ɗaliba ƴar Shekara 3 a Jahar Akwa Ibom

Wata Babbar Kotu a Uyo, Jihar Akwa Ibom ta yanke wa wani mutum ɗan shekara 36, Monday Joshua Okon hukuncin kisa sakamakon Shin garkuwa da wata ɗaliba ƴar shekara 3 a makarantar Mbierebe Obio da ke Ƙaramar Hukumar Ibesikpo Asutan.

An kama Okon ne a kan hanyar sa ta zuwa sayar da yarinyar a Aba, Jihar Abia.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Okon Okon ne ya yanke hukuncin a jiya Juma’a bayan ya kama Okon, mazaunin Ekpene Ukpan da ke Ƙaramar Hukumar Nsit Ibom da laifin yin garkuwa da yarinyar.

An yanke wa Okon, mai aure da ya’ya 2 hukuncin kisan je tare da wata Cecelia Thompson Ebong wacce a ka yanke mata hukuncin shekara 5 a gidan yari, bayan da ita ce ta taimaka masa wajen sace yarinyar, da kuma riƙe masa ita a cikin babur mai ƙafa uku su ka nufi Aba domin haɗuwa da mai saya da ya ke jiran su.

Ya amsa laifin sa a gaban ƴan sanda cewa ya yi garkuwa da yarinyar ne tun 20 ga watan Yuli, 2018 lokacin a na bikin yaye ɗalibai a makarantar su, inda ya sace da kuma ajiye yarinyar tsawon kwanaki uku a gidansa kafin ya tafi da ita Aba, inda a hanya dubun sa ta cika.

Da ya ke yanke hukuncin, Mai Shari’a Okon ya ce abin takaici ne har yanzu mutane sun ƙi dena ta’adar sata da kasuwancin ɗan’adam, duk da ƙoƙarin gwamnati na daƙile mummunan halin.

Inda ya bada umarnin a rataye Okon har sai ya daina numfashi, ita kuma Cecelia a ɗaure ta shekaru biyar a gidan yari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram