Abun Baƙin Ciki: Mutanen Gari Sun Hana Sojoji Kama Mai Sayar Da Bindigogi A Jahar Filato

A jiya Asabar ne dai al’ummar ƙauyen Vom da ke lardin Vwang a Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu su ka hana sojojin rundunar ‘Operation Safe Haven’ kama wani da a ke zargin da kasuwanci da kuma haɗa bindigogi.

Ishaku Takwa, jami’in yaɗa labarai na rundunar ne ya baiyana haka a wata sanarwa a jiya Asabar a garin Jos.

A cewar Takwa, mutanen garin kawai sai su ka fito da yawa su ka riƙa jifan sojojin da dutsina da sauran su domin su hana a kama wanda a ke zargin.

Ya ce wani bayanin sirri ne rundunar ta samu da ga majiya mai tushe, shi ne dakarun su ka haɗu su ka kai simame da sanyin safiyar Asabar ɗin domin su cafke wanda a ke zargi.

Takwa ya ƙara da cewa duk yunƙurin da sojojin su ka yi na su kwantar wa da ƴan garin hankali bai yiwu ba, inda su ka harzika su ka riƙa jifan dakarun da dutsina da makamai masu haɗari, inda ya ce jami’an sojin sun nuna ƙware wa wajen kin tunzuri da hasala.

Jami’in yaɗa labaran ya ce domin ka da abin ya haifar da ɗa maras idanu, sai kwamandan rundunar, Ibrahim Ali, ya bada umarnin janye sojojin ma gaggawa.

“mu na alla-wadai da wannan ta’ada ta hana mu mu kama mai laifi. Amma mu ma masu gargaɗin al’umma a kan matsalar da ɓoye mai laifi za ta haifar a cikin al’umma,” in ji Takwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram