In Har APC Bata Yi Hankali Ba To Ga Ta Can An Zubar A Kwandon Shara – In Ji Sanata Babba Kaita

Dan Majalisar Dattawa a Najeriya mai wakiltar yankin Daura a jahar Katsina, Sanata Ahmad Babba Kaita, ya koka kan yadda jam’iyyarsa ta APC ke fama da takun saka a tsakanin yayanta.

Babba Kaita ya bayyana haka ne a yayin wata fira da yayi da kafar sadarwa ta DW a ofishinsa.

KARANTA KUMA: Yansanda Sun Kai Samame A Maboyar Wani Kasurgumin Dan Fashin Daji A Katsina

Sanatan ya ce rashin adalci da son zuciya da karfa-karfa da jam’iyyar APC ke yi zai iya kawo mata matsala babba musamman idan aka yi la’akari da yadda al’umma suka waye game da sha’anin zaben abinda suke so.

Sanata Kaita ya yi tsokaci kan yadda wasu jahohin suka gudanar da zaben shugabaninsu ba tare da yin abinda ya kamata ba inda ya ce duk yawanci sun yi dauki dora ne ga mukaman.

Bubba Kaita ya kara da cewa in ba a dage aka gyara ba to ga APC ga ta can cikin kwandon shara wandda ba a fatar haka a cewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram