Jami’an Tsaro Sun Ƙwato Shanu 300, Sun Kashe Ƴan bindiga Da Dama A Niger

Ƴan bindiga da dama da ba’a san ko nawa bane dake addabar Ƙaramar Hukumar Magama ta Jahar Niger sun haɗu da gamon su a hannun Jami’an tsaro na Haɗaka a Jahar.

Jami’an tsaron haɗin gwuiwa da Ƴan sakai sun zagaye ƴan bindigar, tare da kashe wasu wanda sukayi ƙaurin suna wajen kaiwa mutane hare-hare a Al’ummomin Munya da Mariga.

A cewar wata majiya wanda ta buƙaci a sakaye sunan, jami’an tsaron da ƴan sintiri har yanzu suna a cikin dajin, tare da kashe ƴan bindigar, ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Wakilin majiyar mu ya shaida cewar an ƙwato sama da shanu 300, daga ragargazar ƴan bindigar a Ƙananan Hukumomin.

An tattara cewa a Karamar Hukumar Mariga, Dakarun soji na Atilari na Birget ta 31 sun samu nasarar kora ƴan bindigar da yawansu a Chikarumbu da Mahoro ta Gulbin Boka tare da ƙwato shanu 200.

Shugaban Ƴan Sintiri a Mariga Saidu Bello yace ƴan bindigar tuni suka tarwatsa al’ummomin, tare da tafiya da Shanun su, inda ƴan sintiri suka yi shiri suka bi bayan su.

Ya ƙara dacewa Sojoji da ƴan sintiri sun yiwa ƴan bindigar kwantan ɓauna a lokacin da suke farmakar Maraba Dandaudu tare da kashe wasun su da dama.

A lokacin da wakilin Majiyar mu ya tuntuɓi Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Wasiu Abiodun yace lamarin ya faru a Mariga da Mashegu, amma bai sanar da yanayin nasarar ba, yana mai cewa aikin na haɗaka da jami’an tsaro da Ƴan Sintiri, don haka bashi da dama ya faɗi wani abu.

Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu da Tsaron Cikin Gida Emmanuel Umar ya Tabbatar da lamarin yana mai cewa ya faru ne a Mariga da Magama, kuma zai shirya taron Manema Labaru a gobe (Litinin) domin sanar da nasarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram