Yansanda Sun Kai Samame A Maboyar Wani Kasurgumin Dan Fashin Daji A Katsina

Rundunar Yansanda a jahar Katsina ta ce ta samu nasara kashe wasu yan fashin daji 4 bayan jami’anta sun bi bayansu a yayin da suka je sata a garuwan ‘Yan mama da ke karamar hukumar Malumfashi da kauyen Tugu-gari da ke karamar hukumar Matazu.

Kakakin rundunar SP Gambo Isah ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Assabar din da ta gabata a farfajiyar hedikwatar su da ke Katsina.

Kalli rabarin cikin hoton bidiyo a nan kasa.

SP Gambo, har ila yau ya ce rundunar ta kai samame a dazukan Hakkin-biri da Yelawa a karamar hukumar Danmusa a wata maboyar wani gasurkumin dan ta’adda da ake kira “Na Iraki” suka batattake su tare da Kwato shanun sata da babura biyu da suke amfani da su su yi sata.

KARANTA KUMA:Abun Baƙin Ciki: Mutanen Gari Sun Hana Sojoji Kama Mai Sayar Da Bindigogi A Jahar Filato

Ya ce kuma jami’an na su sun kone maboyar kafin su baro wurin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram