Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya kaddamar da aikin gina tituna a garin Garo da makwaftan karamar hukumar Kabo da ke jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar, wanda kuma ya rabawa manema labarai a Kano ranar Lahadi.
Gwamna Ganduje ya samu wakilcin kwamishinan kananan hukumomi da masarautu Murtala Garo, tare da rakiyar kwamishinan ayyuka da raya ababen more rayuwa Injiniya Idris Wada, a wajen bikin kaddamar da aikin gina titin a ranar Asabar.
Garo ya bada tabbacin gwamnatin Ganduje cewa za ta yi aiki ba dare ba rana domin inganta ayyukan more rayuwa a yankunan karkara.
“Akwai hanya mai nisan kilomita 18 data tashi daga Kanye-Kabo zuwa Dugabau, wacce ta ratsa unguwanni takwas daga cikin Unguwani goma na karamar hukumar Kabo. An fara aikin ne a cikin shekarar 2018 kuma an watsar da rabin aikin gina hanyar.
“Sai dai an soke kwangilar ne bayan gina kilomita 9. Inad aka sake ba da kwangilar don kammala sauran kilomita 9. Wanda jimlar kudin kwangilar ya kai Naira biliyan 1.6.
“Akwai kuma wani aikin titin a cikin garin Kabo, wanda adadinsa ya kai nisan kilomita 3.9, akan kudi sama da Naira miliyan 800.
Ya ce idan aka kammala aikin zai saukaka zirga-zirgar ‘yan kasa wajen yin safarar amfanin gona daga kauyukan da al’ummar suke zuwa manyan kasuwanni a fadin jihar.
“Masana sun yi imanin cewa, idan aka kammala aikin, zai taimaka matuka wajen zirga-zirgar amfanin gona a tsakanin al’ummar baya ga saukaka zirga-zirgar mutane ba tare da wata tangarda ba.
“Wannan aikin, kamar irin wannan ayyuka a tsakanin al’ummomin karkara da dama a jihar, ya saba da ikirari marasa tushe da wasu mutane ke yi cewa, an yi watsi da al’ummomin karkara wajen samar da ababen more rayuwa na wannan gwamnati domin ana iya ganin irin wadannan ayyuka a wasu wurare,” in ji shi.