Jami’an tsaro aSudan sun harba hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zangar adawa da ƙarin farashin burodi da man fetur.
BBC Hausa ta rawaito cewa an gudanar da zanga-zanga a faɗin Sudan.
Masu zanga-zangar sun ce an yi amfani da harsashi a birnin Damazin da ke kudu maso gabashin kasar.
A ranar Lahadi, farashin burodi ya karu da sama da kashi 40, haka ma an kara kudin man fetir.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ɗaya bisa uku na yawan al’ummar Sudan na dogaro ne da tallafi.
Matsalar ta ƙara ƙamari tun juyin mulkin bara wanda ya sa masu bayan da tallafi suka dakatar da tallafawa ƙasar.