Da Dumi-Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Hallaka DPO Da Wasu Jami’an Tsaro 6 A Jahar Neja

Akalla jami’an tsaro bakwai ne da suka hada da jami’in dan sanda mai kula da yankin Nasko Suka rasa rayukan su, da ke karamar hukumar Magama a jihar Neja, a ranar Talatar da ta gabata.

Jaridar Daily trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na rana.

Yan bindigar da suka yi yunkurin kai hari a Nasko, jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda, sojoji da ‘yan banga na yankin sun mayarmusu da wuta.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce DPO, da wasu ‘yan sanda biyu, da ‘yan banga hudu sun rasa rayukansu a yayin artabu da bindigar.

Abiodun ya ce, “A ranar 15/03/2022 da misalin karfe 1300, ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda sun mamaye kauyen Nasko, karamar hukumar Magama ta jihar Neja.

“Nan da nan DPO Nasko ya tura jami’an ‘yan sanda tare da ‘yan banga inda suka yi artabu da ‘yan bindigar a wani mummunan artabu inda aka kashe wasu ‘yan bindigar, wasu kuma sun tsere da harbin bindiga. Sai dai kuma abin takaicin shi ne, a yayin fafatawa da ‘yan bindigar, DPO da wasu ‘yan sanda biyu, da ‘yan banga hudu sun rasa rayukansu.”

Ya ce, Kwamandan yankin, Kotangora, ya tsara shirin karfafa gwiwa tare da jami’an soji zuwa yankin domin dakile tabarbarewar doka da oda.

Ya ce rundunar ‘yan sandan ta jajantawa iyalan jami’anta da ‘yan banga da suka rasa rayukansu a wannan mummunan lamari, tare da tabbatar wa da jama’a cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen dakile ayyukan ta’addanci a fadin jihar ta Neja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram