Karamar hukumar Ungogo a jihar Kano ta ware filaye 18 ga wasu masu fama da cutar kuturta a wani sabon tsarin da hukumomi suka tsara.
Karamar Hukumar ta ce hakan ya biyo bayan korafin da mazauna unguwar Yadakunya su kayi, inda asibitin kuturta ya ke kan cewa za su iya kamuwa da cutar saboda karuwar masu fama da cutar, hakan ya sa aka mayar da majinyata zuwa unguwar Zaura Kadage.
Shugaban karamar hukumar Ungogo, Engr. Abdullahi Garba Ramat ne ya bayyana haka a karshen makon da ya gabata, inda ya ce an raba filaye 18 ga majinyatan masu cutar kuturta kyauta.
Da yake magana jim kadan bayan baiwa majinyatan masu cutar kuturta kyautar takardar mallakar filaye, Ramat ya ce matakin ya zama dole don magance koke-koken mazauna garin Yadakunya.
Ya bayyana cewa za a kuma samar da ababen more rayuwa kamar wutar lantarki da rijiyoyin burtsatse a tsarin domin saukaka kalubalen marasa lafiyar.
Sai dai shugaban ya ce a halin yanzu yana jiran amincewar gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje na ya fara kafa gine-gine don raya yankin da gine-gine da kuma hada wadanda abin ya shafa da iyalansu.
Da yake tsokaci game da wannan ci gaban, Sarkin Kutare na Kano, Malam Isiyaku Muhammad ya yaba wa shugaban karamar hukumar bisa abin da ya bayyana a matsayin alheri, inda ya ce sama da iyalai 16 ne suka amfana da filayen kyauta.
Muhammad ya bayyana fatansa cewa wannan karimcin zai taimaka matuka wajen magance kalubalen da masu fama da cutar kuturta ke fuskanta a Kano.
Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar kyautar wannan filin, Nafi’u Isiyaku ya ce kafin a samu ci gaba, masu fama da kuturta na zama a gidajen katako wanda hakan yana ba su damuwa sosai.
Nafi’u ya yabawa Engr. Abdullahi Garba Ramat ya yi masa godiya, kamar yadda ya roki shugaban da ya samar da rijiyar burtsatse a yankin kamar yadda ya yi alkawari.