NCC Zata Haɗa Gwiwa Da CBN Domin Yaƙar Damfara A Yanar Gizo

Hukumar Sadarwa ta Ƙasa, NCC da Babban Bankin Ƙasa, CBN za su haɗa gwiwa wajen yaƙar damfara ta yanar gizo domin ita ce babbar barazana ga harkokin kuɗi ta yanar gizo.

Daraktan Sashin Kula da Masu Amfani da Kaya, Efosa Idehen ne ya baiyana hakan a wajen wata gasar muhawara ta Makarantar Sakandare domin tunawa da Ranar Mai Amfani da Kaya ta Duniya.

Idehen ya ce taron zai ilimantar da masu amfani da kaya 2qjen guje wa damfara ta yanar gizo da kuma wayar wa da matasa kai wajen amfani da hanyoyin hada-hadar kuɗi ta yanar gizo.

Ya ce CBN ta baiyana yadda damfara ta yanar gizo ke sanya gwamnati asarar maƙudan kuɗaɗe.

Ya ƙara da cewa CBN ta tabbatar da cewa damfara ta yanar gizo ce babbar barazana ga harkokin kuɗaɗe ta yanar gizo, inda ya ƙara da cewa shi ya sa aka kirkiro da wasu hanyoyi domin magance ta’adar.

Da ga cikin hanyoyin, a cewar sa, akwai katin cire kuɗi, NIBBS da kuma hanyar hada-hadar kudade ta nan take da kuma ta wayar salula.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram