Wani Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutane 11 Akan Hanyar Zaria- Kaduna

Akalla mutane 11 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Zaria zuwa Kaduna da yammacin ranar Asabar.

An tattaro cewa hatsarin ya afku ne a lokacin da wata mota kirar Toyota Carina mai lamba KTL 251QG, ta rasa iko a kusa da Kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli dake Zaria, bayan da ta taka shingen rage gudu.

Kwamandan sashin kiyaye hadurra na tarayya da ke Zariya, Abubakar Tatah Murabus, wanda ya tabbatar da faruwar hatsarin ya ce an kwashe dukkan wadanda abin ya shafa zuwa dakin ajiyar gawa.

Ya kuma dora alhakin faruwar hatsarin a kan sanya mutane fiye da kima da kuma gudun wuce gona da iri.

Ya ce motar mai kujeru biyar da ta taso daga Kaduna zuwa Bakori a jihar Katsina, cike take da mutane 11.

“Hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar da misalin karfe 2 na rana a Tariyar Sarki kusa da Kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli Zariya.

“Don haka ne muke gargadin direbobi da su daina dabi’ar cunkusa fasinjoji fiye da kima.

“Kuna iya tunanin wannan motar da aka so daukar mutane biyar ciki har da direban ta dauki mutane goma sha daya, kuma an ce direban ya wuce gona da iri duk da yawan mutanen da ke cikin motar dole idan aka samu matsala a rasa rayuka,” in ji shi.

Inda ya bayyana sunan direban da Musa Iliyasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram