KEDCO Tayi Kira Ga Al’umma Dasu Ƙara Haƙuri Kan Ƙarancin Wutar Lantarki Da Aka Samu

Hukumar gudanarwar kamfanin rarraba hasken Lantarki a Kano (KEDCO) ta baiwa abokan huldarsu hakuri sakamakon karancin wutar da ake fuskanta a jihohin Katsina, Kano, da Jigawa.

Mai magana da yawun hukumar Ibrahim Sani Shawai a cikin wata sanarwa da ya fitar Mai dauke da sa hannunsa, yace matsalar karancin lantarkin ba iya jihohin sama bane, domin Kuwa a kasa baki daya ma irin wannan Matsala ake fuskanta.

Shawai ya ce karancin wutar nada nasaba da koma baya da aka samu wajen rabata, daga kamfanonin da suke tunkudo wutar ga kamfanoni irin nasu.

Ya kara da cewa Karancin sinadarin Gas, shi ma ya taimaka wajen raguwar wutar lantarkin, Wanda kuma yanzu haka suna bakin kokarinsu wajen shawo kan wannan matsala.

Shawai ya kuma sha alwashin cewa kamfanoninsu zasu ci gaba da aiki ba dare ba Rana wajen tabbatar da matsalar ta zo karshe.

Majiyar Jaridar Jakadiya ta rawaito cewa yanzu haka jihohin uku na ci gaba da kokawa kan karancin wutar da suke fuskanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram