Sanatocin APC Zasu Gana Da Bola Tinubu Kan Rikicin Jam’iyyar

Rikicin Jam’iyyar APC: Sanatocin APC za su gana da Bola Ahmed Tinubu

Ƴan Majalisar Dattijai na jam’iyar APC za su gana da jagoran Jami’yar na ƙasa, Bola Tinubu a yau Laraba da ƙarfe 2:30 na rana.

Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmad Lawan ne ya baiyana haka a wata wasiƙa da ya karanta a farkon zaman majalisar na yau.

Jagoran majalisar, Sanata Yahaya Abdullahi (Kebbi ta Arewa), shi ne ya sanya hannu a wasiƙar.

“Akwai ganawa da jagoran Jami’yar APC, Snata Bola Ahmed Tinubu a yau 16 ga watan Maris 2022, in ji Lawan.

Za a yi ganawar ne a ɗakin taro na shugaban majalisar.

Duk da cewa ba a san batutuwan da za a tattauna a ganawar ba, wakilin mu ya jiyo cewa ba ta rasa nasaba da rikon shugabanci da ya dabaibaye APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram