Wutar Lantarki Ta Inganta A Karkashi Mulkin Buhari – Inji Buhari Bashir Ahmed

Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari akan Sabbin Kafafen Sadarwa na Zamani Bashir Ahmed ya yi jawabi akan lalacewar wurin Samar da Hasken Wutar Lantarki na Ƙasa.

 

Ahmed ya cigaba da cewa, Wutar Lantarki ta inganta a Ƙarƙashin mulkin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

KARANTA KUMA:Da Dumi-Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Hallaka DPO Da Wasu Jami’an Tsaro 6 A Jahar Neja

Ya bayyana cewar rugujewar wajen samar da wutar, ya samu ne sakamakon rashin ƙarfin ɓangarorin tura hasken wutar lantarkin da Wannan Gwamnati ta gada a Gwamnatin data gabata.

A cikin saƙon Twita daya tura, Hadimin Shugaban Ƙasar ya bayyana cewar Najeriya ta fuskanci Lalacewar wurin a Shekarar 2020, da Lalacewar wurin sau 42 a Shekarar 2010.

A cewar Ahmad “a lokacin da muke shirye domin tattaunawa akan wannan matsala, dole musan cewa ɓangaren samar da wutar lantarki ya inganta a Ƙarƙashin wannan Gwamnatin.

“Lalacewar wajen samar da Hasken wutar lantarki ya faru ne a dalilin rashin ingantattun kayayyakin kula da wutar lantarki.

Lalacewar wajen samar da Hasken wutar lantarki ya afku ne da misalin ƙarfe 10.40.na safe na ranar Litinin, wanda hakan ya haddasa ɗaukewar wutar a wasu sassan Najeriya.

Ƙasa da awanni 24 bayan wannan lamarin, wasu sassan Ƙasar a ranar Talata sun sake fuskantar rashin wutar lantarki bayan faɗuwar wani ɓangaren wutar.

Mr Felix Ofulue, Shugaban dake Hula da Sadarwa na Kamfanin Wutar Lantarki ta Ikeja ya tabbatar da wannan lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa a Lagos.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram