Buni Ya Dawo Najeriya, Ya Ɗare Kujerarsa Ta Shugabancin APC

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya ɗare kujerarsa ta shugabancin riƙo na jam’iyar APC bayan dawowarsa da ga neman lafiya a ƙasar waje.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwar da Darakta-Janar na yaɗa labarai na Buni, Mamman Mohammed ya fitar a yau Alhamis a Damaturu.

Mohammed ya ce Buni ya yi kira ga ɗaukacin ƴan jam’iya da su kwantar da hankali su kuma zama masu bin doka.

A cewar sa, Buni ya yi kira ga ƴan jam’iya da su manta da rikicin kwanannan da ya faru, su kuma sanya babban taron jam’iyar a gaba.

“Nasarar jam’iyar nan itace sama da komai kuka dole ba za ta samu ba sai kowa ya sa hannu da bada haɗin kai,” in ji Buni

Gwamnan ya kuma yi kira ga ƴan jam’iyar da a dena ɓullo da wasu lamura da za su raba wa jam’iyar hankali da sauka da ga kan gwadaben nasara.

Ya kuma yi nasiha da a dai a jin haushin juna, inda ya ce hakan wani bata lokaci ne a ce za a riƙa kullatar juna a kan rikicin shugabancin jam’iyar da ya faru kwanan nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram