Rahotannin dake Fitowa na nuna cewa wata motar bas dauke da mata da yara 53 da ke kokarin tserewa rikicin Rasha da Ukraine ta kife a kusa da garin Pasvalys na kasar Lithuania.
Direban motar yana tuki ne daga kan iyakar Poland da Ukraine zuwa Finland sai ya rasa iko da Motar da misalin karfe 06:00 agogon kasar (08:00 GMT), a cewar tashar talabijin ta kasar Lithuania ta LRT.
An ce akalla mutane 10 ne da suka hada da kananan yara ne suka jikkata. An kai su asibitocin da ke kusa da yankin da lamarin ya faru.
An kai sauran fasinjojin zuwa cibiyar al’adu ta Salociai.
Daya daga cikin fasinjojin ya shaidawa gidan talabijin din cewa: “Ba mu yi barci ba tsawon kwanaki uku kafin faruwar lamarin.
“A daidai lokacin da na ke barci sai motar bas ta kife, ‘yata ta fara kururuwa, nan take , ta fadi daga kan kujerar ta karasa kusa da direban. Mun godeqa Allah, ba ta samu rauni ba.”inji shi