Hukumomi a Mariupol sun ce kusan mutane 30,000 ne suka bar birnin ya zuwa yanzu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Majalisar karamar hukumar ta yi kiyasin cewa sama da mutane 350,000 ne ke ci gaba da samun mafaka a birnin.
Dakarun Rasha sun kewaye birnin mai tashar jiragen ruwa kuma an yi ta luguden wuta mafi muni a rikicin a yankin kafin su kwace Iko da shi.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton dogayen layukan motocin da suka nufi arewa daga Mariupol, wasu da alamun a cikin an rubuta kalmar “yara” da harshen Rashanci.
Jami’an Ukraine sun ce mazauna birnin sun fake a wasu wurare a cikin birnin sakamakon ruwan wutar da Rasha ke yi musu.
Majalisar birnin ta kara da cewa ana ci gaba da gudanar da aikin tantance adadin wadanda suka mutu sakamakon harin da aka kai a gidan wasan kwaikwayo na Mariupol inda sama da mutane 1,000 – galibi mata da kananan yara – suka boye a sansanin