Na Taba Sadaukar Da Rayuwata Ga Yan ta’adda Saboda A Samu Tsaro A Jahar Katsina – Mustapha Inuwa

Sakataren Gwamnatin Jahar Katsina Mustapha Inuwa, ya ce ya taba tarar aradu da ka inda ya sadaukar da rayuwarshi ga yan ta’adda domin sa shawo kan matsalar tsaro a jahar Katsina.

Mustapha Inuwa ya bayyana haka ne a yayin da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Larabar nan a dakin taro na yan jarida da ke gidan gwamnati.

KARANTA KUMA:Abba Kyari Yayi Baz Day Nashi A Hannun Hukumar NDLEA

An tambayi Sakataren Gwamnatin ne cewa mutane da dama suna alakanta shi da matsalar tsaro da jahar ke fuskanta, shin yayn abin ya ke? Sai ya amsa da newa mutane ba za a raba su da kalaman batanci ba ya kara da cewa kuma ma da suke wannan maganar shi har sadaukar da rayuwarshi ya yi domin a samu tsaro a Katsina.

Ya ce lokacin da gwamnatin jahar na neman ta yi sasanci shi ne ya je neman yan ta’addan cikin daji don su zo su gana da gwamma su aje makamansu.

Inuwa ya ce a lokacin har sai da ya nemi kwamishinan yansanda na wancan lokacin su tafi tare amma ya ki zuwa.

Ya ce daga karshe da ya je cikin dajin wurin su shahararren dan ta’addan nan mai suna Dangote ya ga sun ki yarda su zo wajen sasanci cewa ya yi ya yarda su rike shi in shi Dangoten ya je ya dawo lafiya su sake shi in kuma sun ga bai dawo ba to su kashe shi kawai.

Mustapha Inuwa dai yana daya daga cikin mutanen da suka fara nuna sha’awarsu ta son fitowa takarar Gwamnan jahar ta Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram