Antoni-Janar na Ƙasa Abubakar Malami kuma Ministan Shari’a a ranar Alhamis yace bazai ajiye muƙamin sa ba.
Malami yace sai yaga ƙarshen wa’adin mulkin sa a watan Mayu na Shekarar 2023.
Malami ya bayyana haka, a lokacin da yake bada jawabin buɗe wa a wani taro, da Ƙungiyar Ma’aikatan Shari’a suka shirya.
“Mutane da dama da suka dogara ga jin bayanai na Ƙarya, suna cewa Malami ya ajiye muƙamin sa a Matsayin Antoni-Janar, kuma Ministan Shari’a, ana ganin sa a ofishin sa yana gudanar da aikace-aikace, ciki harda halartar taron Majalisar Zartaswa ta Ƙasa a jiya, kuma yanzu yana buɗe taro a matsayin Antoni-Janar na Kasa.
“Akwai ƙarshen komai. Wa’adina na Mulki har yanzu bai ƙare ba. Ina fatan inyi kyakkyawan ƙarshe,” inji shi.
Jita-jita na cigaba da yawo cewa Malami zaiyi takarar Kujerar Gwamnan Jahar Kebbi a Shekarar 2023, amma ɗan Shekaru 54 bai bayyana ra’ayin sa ba akan haka.