Jakadiyar Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce bai kamata ƙasashen Afrika su zama ƴan ba-ruwanmu a yaƙin Rasha da Ukraine ba.
Jakadiyar Linda Thomas-Greenfield,
ta ayyana haka ne a yayin wata hira da BBC, ta yi da ita ta ce, ƙuri’ar da aka yi a babban zauren majalisar makonni biyu da suka gabata kan ƙin amincewa da kutsen da Rasha ta yi wa Ukraine, ta ce ƙasashe 17 sun ƙi ɗaukar ɓangaren sai kuma ƙasashe takwas sun ƙaurace wa jefa ƙuri’ar baki ɗaya.
KARANTA KUMA:Kimanin Mutane 30,000 Sun Tsere Daga Mariupol
Ta ce babu batun zama ƴan ba-ruwanmu a wannan lamari kuma wannan yaƙin ba yaƙin caccar baka bane tsakanin ƙasashen Yamma da Rasha.
Ms Greenfield ɗin kuma ta ce kasarta za ta mara baya ga kudurin Afirka Ta Kudu na shiga tsakani a yakin na Ukraine.