Ƴan bindiga Sun Bankawa Gidan Shugaban Ƙungiyar Ohanaeze Wuta A Jahar Imo

A safiyar ranar Asabar ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari gidan shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Farfesa George Obiozor, da ke Awo-Omanma a karamar hukumar Oru ta Gabas a jihar Imo.

PUNCH ta ruwaito cewa maharan da suka isa gidan shugaban Igbo a cikin motoci sun jefa bama-bamai a gidan.

An gano cewa Obiozor baya gida lokacin da aka kai wa gidan nasa wannan mummunan harin.

Wata majiya ta ce, “An kona gidan Farfesa George Obiozor. Na’urorin daukar hoto na CCTV sun dauki harin. Mun godewa Ubangiji lokacin da suka zo Farfesa baya gida.”

Obiozor har yanzu bai mayar da martani game da harin ba amma daya daga cikin shugabannin kungiyar Ohanaeze Ndigbo, wanda ya fi son a sakaya sunansa, ya ce ya kira Obiozor ya jajanta masa kan lamarin.

Kazalika ya ce, ya na kira ga ‘yan sanda da su kamo wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.

Kakakin ‘yan sanda a jihar Imo, Micheal Abattam, har yanzu bai mayar da martani kan wanan bincike da aka yi kan harin da aka kai gidan Obiozor ba.

Harin da aka kai a gidan Obiozor, ya zo ne a cikin daren da aka kona hedikwatar ‘yan sanda reshen Umuguma da ke karamar hukumar Owerri ta Yamma ta jihar tare da kashe wasu ‘yan sanda biyu da kuma da kona motoci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram