Korona Ta Sake Barkewa A China Ta Kashe Mutum 2

An sake samun bullar cutar sarkewar numfashi, wato korona mai tsanani a kasar China inda kuma ta hallaka mutane 2 a kasar.

Hukumomin kasar ta China sun bayar da sanarwar cewa, wannan shi ne karon farko da cutar ta kashe wani dan kasar tun cikin watan Janairun 2021.

KARANTA KUMA:Don In Kare Kaina, Shiyasa Na Shararawa Matar Obiano Mari – Cewar Bianca Ojukwu

Ya zuwa yanzu dai mutane kimanin dubu 4 da 638 ne cutar koronar ta hallaka a kasar ta China tun bayan bullarta ta farko a wajen karshen shekarar 2019.

Sake bullar wannan cuta dai zai matukar tayar da hankalin duniya bayan lafawar da ta yi na dan wani lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram