NAFDAC ta Ƙone Lalatattun Magangunan Miliyan 50 A Jahar Sokoto

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa a ranar Juma’a ta lalata magungunan jabu da suka wuce naira miliyan 50 a jihar Sokoto.

An kona kayayyakin ne a wurin juji na Kwannawa kusa da tsohon ofishin gidan waya a karamar hukumar Dange-Shuni.

Babban jami’in hukumar ta NAFDAC na jihar, Mista Adamu Garba, ya ce atisayen na daya daga cikin kokarin da hukumar ta saba yi na tsaftace kasar daga jabun kayayyakin da wa’adin su ya kare da sauran kayayyakin da ba a kayyade su ba daga yaduwa.

Garba ya bayyana jabun magungunan da wa’adin su ya kare da kuma kayan masarufi a matsayin babban hatsari ga rayuwar dan Adam.

“Kayayyakin da aka lalata a yau sun hada da na jabu/ kayan abinci marasa inganci da wa’adin su ya kare, kayan kwalliya da kayyakin da hukumar NAFDAC ta kama yayin da wasu masu shaguna suka mika wuya bisa radin kansu.

“Wannan atisayen na hadin gwiwa ne na jama’a da masu zaman kansu tare da masu siyar da kwayoyi, ‘yan kungiyar kamar yadda kashi 80 cikin 100 na kayayyakin da aka lalata sun mika wuya ne bisa radin kansu,” inji Garba.

Ya bayyana cewa adadin kayayyakin da aka lalata ya nuna cewa hukumar na aiki tukuru don tabbatar da tsaron lafiyar ‘yan Najeriya.

Ko’odinetan jihar ya yabawa masu ruwa da tsaki da jami’an tsaro bisa goyon bayan da suka bayar tare da ba su tabbacin cewa hukumar za ta ci gaba da aiwatar da takunkumin da aka samu.

Sannan ya kara da cewa hukumar ta fara wayar da kan jama’a a fadin jihar kan ayyukan jabun kayayyakin da wa’adin su suka kare, ya kuma bukaci masu siyar da kayayyaki, masu kera kayayyaki da masu amfani da su da su bi ka’idojin da aka gindaya.

Mista Emmanuel Andrew, mataimakin darakta, shugaban bincike kuma memba a kungiyar Kartakwana ta kasa ta NAFDAC, ya ce an yi kokarin kawar da jabun kayayyakin, da wa’adin aikin su ya kare da kuma wadanda ba su yi rajista ba daga kasuwanni.

Andrew ya ce ya je Sokoto ne domin sa ido kan ayyukan masu sayar da magunguna da kuma shagunan sayar da magunguna domin hada kai da hukumar ta hanyar mika haramtattun kayayyaki.

Ya jaddada muhimmancin kokarin hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki a fafutukar kare lafiyar mutane.

NAN ta rawaito cewa atisayen ya samu halartar mamban hukumar gudanarwa ta NAFDAC, Alhaji Tukur Sarkin Fada Tambuwal da Alhaji Abdullahi Dikko, Daraktan Bincike da Kididdiga na Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Sakkwato.

Sauran sun hada da Alhaji Nasiru Abdu daga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Sakkwato (SEMA) da kuma wakilin masu sayar da magunguna, Mista Ogbu Batholomew.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram