Ƴan sanda Sun Harbe Ƴan Tawayen IPOB A Mahaifar Gwamnan Uzodimma

An kashe wasu da ake zargin ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ne a wani artabu da ‘yan sanda suka yi da su a garin Omuma, mahaifar Gwamna Hope Uzodimma, da sanyin safiyar Lahadi.

A cewar CSP Mike Abattam, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar Imo, an kashe ‘yan bindigar ne a wani hari da suka kai ofishin ‘yan sandan Omuma da ke karamar hukumar Oru ta Gabas a jihar.

“A ranar 20 ga Maris, 2022 da misalin karfe 0300, wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar ‘yan asalin yankin Biafra ne da kungiyar ‘yan ta’adda ta Eastern Security Network sun zo da yawa dauke da na’urorin fashewa daban-daban zuwa ofishin ’yan sanda na Omuma suna harbe-harbe. ‘yan sanda suka fatattake su cikin gaggawa.”

“Jami’an ‘yan sandan sun kama ‘yan bindigar ne da muggan makamai, inda a nan take aka kashe hudu daga cikin ‘yan bindigar , yayin da sauran suka tsere zuwa cikin daji bayan da suka samu gagarumar nasara a kan su, inda da dama daga cikinsu suka samu raunuka daban-daban.”

Ya ce an kwato layuka da wasu na’urorin fashewa daban-daban da ba a san ko mene ba, daga Yan bindigar da aka kashe.

Rundunar ‘yan sandan, a cewarsa, a halin yanzu tana binsamun Yan Bindiga har Cikin daji domin kamo sauran da suka gudu.

Lamarin dai ya faru ne sa’o’i 24 bayan wasu ‘yan bindiga sun kai harin bam a hedikwatar ‘yan sandan da ke Umuguma na karamar hukumar Owerri ta Yamma a jihar, inda suka kashe jami’ai biyu.

Har ila yau, a ranar Asabar din da ta gabata, wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Farfesa George Obiozor, a unguwar Awomamma, a karamar hukumar Oru ta Gabas.

Da yake tsokaci a kan lamarin, Uzodimma ya zargi ‘yan siyasa masu ra’ayin rikau, wadanda ya ce nan ba da jimawa ba za a farauto su.

A cikin wata sanarwa da da kansa ya sanya wa hannu, Gwamna Uzodinma ya yi nadama kan yadda ‘yan siyasa masu ra’ayin rikau da suka yi imani da tashin hankali ba su tuba ba, duk da kiraye-kirayen da ake yi na yin hakan.

Ya koka da yadda ake tashe-tashen hankula a tsakanin wasu ‘yan siyasa a jihar, ya kuma yi gargadin cewa gwamnati ba za ta lamunci irin wannan ta’addanci ba.

A cewarsa, “Lokacin wadanda suke tada irin wannan tarzoma a jihar ya wuce. Za mu farauto su don fuskantar cikakken hukuncin da doka ta tanada

Uzodinma ya yi mamakin dalilin da ya sa ‘yan bindigar za su kai hari gidan wani mutum wanda ba dan siyasa ba ne, dan jiha ne mai fafutukar kare al’ummar Igbo baki daya.

Ya Kuma kara da cewa, abin kunya ne a ce masu daukar nauyin wannan rikici da masu tayar da kayar baya sun kai mummunan hari kan wani mutum da ba shi da laifi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram