Kungiyoyin masu zaman kansu 286 tare da magoya bayansu sun ce suna goyon bayan Sakataren Gwamnatin Jahar Katsina Mustapha Inuwa ya zama gwamna.
Wannan goyon baya ya fito ne daga bakin kungiyoyin da magoya bayansu a yayin wani taro da suka yi don nuna ma Sakataren Gwamnatin Mustapha Inuwa matsayarsuta son ya ci gaba da amsa kiran da al’ummar jahar na bukatars gare shi da ya tsaya takarar Gwamnan.